Kimiya Da Fasaha

Wata Sabuwa: Nan Da Shekaru Kaɗan Za’a Fara Yiwa Mutane Dashen Kai (Head Transplant)

Spread the love

Nan Da Shekaru Kaɗan Za’a Fara Yiwa Mutane Dashen Kai (Head Transplant), misali za’a iya guntule kan wani a jona a wani mutumin kuma suyi rayuwa babu matsala kamar yanda wani kwararren likita ɗan kasar Italia mai suna Dr. Sergio Canavero ya wallafa a cikin littafinsa mai suna “Head Transplantation and the Quest for Immortality.”

Haka zalika likitan ya samar da wani bangaren bincike na musamman domin gano dalilan da suke sawa dukkan abubuwa masu rai suke mutuwa tare da tunanin kawo maslaha (maganin da zai iya hana mutuwa), haka zalika likitan yana bincike tare da ɗaruruwan masana a birnin Italiya domin samar da hanyar ƙarawa mutane tsawon kwanaki a duniya….

Wani abun mamakin shine bayan jarraba gwada yiwa Aladu dashen kai an samu nasara sun rayu Kuma kowanne a cikinsu ya ci gaba da yin rayuwarsa ba tare da wani kwakkwaran canji ba, haka zalika Aladun sun sake samun wata sabuwar fikira da basira.

Shin zaka iya yarda a cire kan wani abokinka ko ɗan’uwanka a dasa maka? Amma idan aka cire kan mutum ina makomar ilimin da yake cikin kwakwalwarsa?

Wannan ita ce amsar da muke jira daga wajen likitan.

✍️Usman Umar Dagona

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button