Wata Sabuwa: Tarihi ya nuna Garin Suleja sune sukafi cancanta da sarautar Zazzau: Roko El rufa’i
Tarhin sarautar Suleja da masarautar Zazzau Rubutawa: Mairo Muhammad Mudi a shafin ta na RAGAYA a cikin jaridar Leadership
Kafin na fito da kukana a fili a wannan shafin sai na ba da tarihi biyu wadanda suka sa ni ke ganin Suleja sun cancanci sarautar Zazzau da kuma ganin cewa Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El-rufai ne zai share mani wannan hawaye. Tarihi na farkon kan Suleja ne na biyu kuwa kan abinda Malam El-rufai ya taba wa Suleja.
Suleja, ainihin sunan garin shine Abuja wanda sunan ya yi asali ne daga sunan kanin Sarkin Zazzau, Zaria na 60, Kuma Sarkin karshe na Hausawa a masarautar Zaria watau Muhammmadu Makau wanda ya zama Sarkin Zaria a shekarar 1802 amma a lokacin sallar Idi karama, Sarki Makau suna bayan gari suna sallah a ranar, Fulani suka fada masu da yaki suka rufe garin yadda babu hanyar da Sarki Makau da makararrabansa za su koma ciki ga shi babu makamai a hannunsu. Haka Fulani suka kori Sarki Makau ya zo Karau, daganan ya je Kajuru sannan suka yar da zango a Zuba inda daga bisani, Allah Ya yi wa Sarki Makau rasuwa sai kaninsa Abu-Ja ya hau sarauta inda suka share gari tare da taimakon kwarawa suka kafa garin Abuja. Daular Abuja ta kasance mai girma inda daga bisani, shugaban kasa, Janar Murtala Muhammmad a lokacin Sarkin Zazzau na shida, Alhaji Sulemanu Barau, ya nemi garin su ba da wurin kafa babban birnin tarayya, manyan gari suka amince sannan aka sake nemen alfarma da su ba da sunan garinsu Abuja ya zama sunan babban birnin Nigeria, suka sake amincewa. A nan ne aka sakawa tsohuwar Abuja sunan Sarki Suleman ta dawo Sule-ja. Har ila yau Gwamnati ta nemi ta kafa ofisoshinta don gudanar da gina Abuja da wurin zaman maikatan gina birnin, Suleja ta amince ta ba da wuri a cikin garin kamar Hill Top, inda gidan talabijin ta kasa NTA, ta fara gina tasharta. Dawaki, inda FCDA ta ke sannan Field Base inda ma’aikatu da dama suka gina inda ma’aikatansu ke zama.
Tarihi na biyun da za ba ku ya shafi gwamna El-rufai kai tsaye. Mu, na baya mun taso da mamakin koma bayan garinmu sannan bayan filaye da aka karba da ke karkarshin Abuja, babu wani diyya a ku zo a gani sannan wadannan ma’aikata suna ikirarin inda suka fara ya da zangon a Suleja kafin gina Abuja wurin su ne. NTA ma ta tunbuke kayan aikinta ta mayar Abuja amma har yanzun ginin da ya ke a walakance ya mayar da layin GRA da da muke alfahari da shi babu gyara Kuma babu wanda zai gyara tunda sun ce nasu ne. Lokacin an ce wasu ma’aikata sun ce Field Base ma wurinsu su ne.
A nan ne na fara bincike sai na samu labari mai faranta rai cewa ai Field Base ya zama na Suleja don El-rufai ya mayar mata da wurin. Bincike ya nuna cewa Galadiman Zazzau Suleja, Alhaji Rabiu shine ya samu Gwamna El-rufai lokacin yana ministan Abuja ya fada masa irin rashin adalci da ake son a yi wa Suleja ta hanyar karbar Field Base, sai ya yi bincike amma su ma’aikatar sun ce wurinsu ne ba aro aka ba su ba kamar yadda Galadima ya ce. Daganan Malam El-rufai ya ce wa Galadima ko zai iya kawo sheidar cewa aro Suleja ta ba da wurin, Galadima ya ce a ba shi lokaci ya kawo sheida. Daganan aka ce ya je Minna wajen ma’adanan takardu ya yi kwana da kwanaki da ‘kyar ya zakulo takadar shedar da a ka sa hannu cewa aro aka ba su ba kyauta ba. Ana kawo wa Malam, ya sa hannu ya ce a mayar wa Suleja da kayanta. Yanzun haka an mayar da katafaren wannan wurin jami’ar IBB duk da ba a fara komai a ciki ba amma kam hankalinmu ya kwanta da wannan adalci irin na Malam.
Wannan dalilai ya sa na samu kwarin gwiwar fuskatar Malam Nasiru El-rufai adalin gwamna, agogon Sarkin aiki da ya dubi wannan koke nawa, ya dawo mana da martabarmu. Da Sallah fa a ka kori kakaninmu daga Zaria zuwa har Abuja suka sake kafa kasar da ya zan abin so ga kowa da ya taimakawa kasar nan bakidaya saboda haka ina ganin in an koma tarihi aka mai mana da sarautarmu ta Zaria babu aibu ciki kuma adalci kenan.
Fulani sun nuna mana karfi sun kwace mana sarautar mu ta Zaria. Yanzun lokaci ya yi da Hausawa ya kamata su koma gudansu na gado.
Da wannan ni je mika ta’aziya ta a madadin dukanmu mutanen Suleja zuwa ga Mai girma gwamna, da ‘yan’uwanmu na Zaria kan wannan babban rashi da muka yi bakidaya.
A Suleja a kullum muna alfahari da cewa, mu ‘yan Zaria ko da kuwa mulki ba zai dawo hannunmu ba amma muna son duniya ta sani cewa, kakaninmu sun baro gida a dole suka bar wasu ‘yan’uwanmu da iyaye a can suka dawo Abuja(Suleja)da zama.
Kila da za a zurfafa bincike za a kane ‘yan Suleja na da alaka da gwamna Nasiru El-rufai kamar yadda suke da alaka da masarautar Zazzau. A wani bidiyo da na ga aikin da El-rufai ke yi a jihar Kaduna, a cikin ba’a na cewa ‘yan kungiyarmu su ba mu aron Malam suka ce an ki din sai na ce ba su San cewa gobe Suleja za ta iya zama jiha kuma in mun yi bincike za mu iya kawo hujjoji cewa da mu da Malam jininmu daya kuma zai iya dawowa Suleja ya zama mana gwamna muma ya rurusa mana wuri ya yi ta aiki har tsakar dare.
Babu mamaki don cikin dare daya Allah kan yi bature.