Wata Sabuwa Tarihi ya nuna sarki Muhammadu Sanusi Na II na iya Zama Sabon Sarkin Zazzau…
Wani marubuci Kuma masanin Tarihi Mai suna Aldaurawiy4h Yace Fadar masarautar Zazzau da ilahirin mutanen Zazzau yanzu haka sun zura ido su ga wanda za a nada a matsayin Sarkin Zazzau na gaba, bayan rasuwar Mai martaba Shehu Idris. A nan a cikin wannan labarin, zan fada maku wani kyakkyawan dalilin da za iya sawa Muhammadu Sanusi ll ya zama sarki na gaba a zazzau.
Da farko, dalilan da ke yawo kan dalilin da yasa za a nada shi a matsayin sarkin Zazzau saboda; Sanusi ya taba zama Sarki kuma ya fito daga gidan sarauta,
ya yi karatun addini da na Zamani kuma na uku, Sanusi aboki ne ga gwamnan jihar kaduna dalilin da yasa Sanusi zai iya zama sarkin Zazzau shine saboda alaƙar kakannin da ke tsakanin masarautun Kano da Zazzau.
Idan za ku iya tunawa daga tarihin masarautar Hausa, Bawo, ɗan Bayajidda ya haifi ‘ya’ya bakwai, waɗannan 7 bi da bi sun mulki Daura, Kano, Katsina, Zazzau, Gobir, Rano da Garin Gabas. Ana iya ganin Bawo akan lambar plate din Sarkin Daura. Wannan ita ce fadar mai martaba sarkin Daura,
wacce aka yi amannar ita ce hedkwatar asalin jihohin Hausa. Don haka, Kamar yadda tarihi ya nuna, manyan masarautun Zazzau da Masarautar Kano ‘yan uwan jini ne,’ ya’yan sarkin Daura, Bawo. “
Allah Ya gafarta kurakuran Mai Martaba, Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Dr. Shehu Idris kuma Ya ba shi masauki a Aljannatul Firdaus. Kuma Allah Madaukakin Sarki Ya zaba mana mafi alheri a matsayin magajinsa”!