Tsaro

Wata Zanga Zangar Rashin Tsaro Yanzu Haka Tana Gudana A Jihar Neja.

Spread the love

Da sanyin safiyar Yau Talata Matasan Minna Babban Birnin Jahar Neja Sun Amsa kiran Kungiyar Matasan Arewa, Inda Matasa a garin Minna Masu zanga zangar lumana a minna Sunyi Zanga zangar ne Kan Kisan da yan Ta’adda keyi babu gaira babu Dalili a Yan kunan Shiroro, Munya da Rafi dake Jahar.

Masu su zanga Zangar Sun Ziyarci Gidan Maimartaba Sarkin Minna Dr. Umar Faruq Bahago Inda Mai Martaban Ya Tarbesu Kuma Ya musu bayani mai Gamsarwa.

Masu zanga zangar a Neja Har Ilau Sun yi kira ga Gwamnati kan matsalar Fyade da Ya Addabi Jahar a Halin Yanzu.

Sai dai tun Da Sanyin safiyar yau Anjibge Jami’an Tsaro A Koina a Minna Da zummar Sanya Ido kan Masu Zanga Zangar.

Ko a Shekaranjiya Asabar yan Ta’adda Sun Harbi Yan sanda 2 A karamar Hukumar Shiroro ta Jahar Neja, Sai Dai Yan Sandan Sunyi Nasarar Kashe Yan Ta’addan da Kwace makamansu Ranar Asabar da Tagabata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button