Wayewar Hadiza Bala Usman ya taimaki Nageriya da Ma’aikatar NPA ~Sanata Uba sani
Sanatan kaduna ta tsakiya Malam Uba Sani ya Taya Hadiza Bala Usman Murnar sake Samun mukami inda Sanatan ya ke Cewa Ina taya ‘yar uwata kuma tsohuwar abokiyar aikina,
Hadiza Bala Usman murnar sake samun mukamin da ta yi a matsayin Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA).
Sanatan Yace Halinta na wayewa, mutunci da kuma jagoranci mai karfi sun maida NPA tare da samun babban ci gaban ƙasa.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da shiryawa da tsare Hadiza yayin da take ƙoƙarin ta ɗauki NPA zuwa manyan matakai Inji Sanatan
A jiyane dai Shugaba Muhammadu Buhari ya sake sanar da nadin na Hadiza Bala Usman a Matsayin Daraktar tashoshin Jiragen Ruwan Bayan da ta kwashe Shekaru biyar tana Jagorancin Ma’aikatar kafin Samun Mukamin NPA Hadiza itace Shugabar Ma’aikata ta Gwamna El’rufa’i na Kaduna Haka Kuma Itace ta Jagoranci Kungiyar Bring Back Our Girls a Lokacin da Kungiyar Boko Haram Suka sace ‘yan Mata Daliban Makarantar Chibook a Lokacin Mulkin Goodluck Jonathan…