WHO : Korona Barazana Ce Ga Masu Larurori na Kiwon Lafiya.
Daga Haidar H Hasheem Kano
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce annobar corona ta zama babbar barazana ga sauran mutane masu fama da wasu larurori na kiwon lafiya a fadin duniya.
A wani binciken da ta gudanar cikin kasashen duniya 155, hukumar lafiyar ta MDD, ta ce mutane da dama da ke fama da manyan matsaloli na lafiya su ne abin ya fi shafa.
Hakan kuwa na faruwa ne saboda rashin kulawa da ta kamata su samu a wannan lokaci da hankali ya karkata kan yaki da wannan annoba.
Binciken ya gano cewa an dakatar da kulawa da masu cutuka da ke da nasaba da zuciya da kashi 31%, haka su ma masu fama da cutar daji ko Cancer da suka kai kashi 42% lamarin ya shafe su.
Sakamakon binciken ya ce su ma masu fama da cutar sukari ko Diabetes da suka kai 49% ba sa samun kulawa saboda annobar, kamar yadda wadanda ke bukatar kulawar gaggawa da suka kai 31% da ke a cikin adadin.