Lafiya
WHO Ta Yi Kira Ga Gwamnatoci Da Su Tabbatar Cewa Sun Baiwa Likitoci Da Ma’aikatan Jinya Kayan Kariya Lokacin Da Suke Aiki.

Daga Abdul Aziz Muhammad
A cewarta, ya kamata duk wanda zai yi mu’amala da mutumin da ake zargi yana dauke da cutar ya kasance sanye da kayan kariya.
Ma’aikatan lafiya da ke kula da masu korona suna iya daukar cutar ta hanyar shafar wayu ko ruwan da ke fita daga jikin mai dauke da cutar don haka ya kamata su rika sanya kayan kariya, ciki har da rigar kariya da ke rufe mutum daga sama zuwa kasa da abin da ke taimakawa mutum yin numfashi da makarin ido.
Sai dai kayan kariya sun yi karanci a duk fadin duniya saboda matukar bukatarsu da ake yi.