Labarai

Ya Allah ka Kare mana ka Kuma karfafa mana Shugaba Muhammadu Buhari ~Sanata Uba Sani

Sanata Malam Uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya ya taya Shugaba Buhari Murnar Zagayowar Ranar haihuwa sanatan ya rubuta a shafinsa na Twitter Yana Mai Cewa… A yayin bikin cikarsa shekaru saba’in da takwas 78 a Duniya Nima na shiga sahun miliyoyin ‘yan Najeriya masu fatan alheri a duk fadin duniya da jinjina ga Mahaifinmu kuma Jagoranmu, Mai Alamar shedar da baza’a iya musantawa ba kuma Mai alamar aminci da saukin kai, Shugaba Muhammadu Buhari.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da shiryarwa, karewa da kuma karfafa Shugaban mu musamman a daidai Wannan Lokaci da yake jan ragamar kasar nan cikin wadannan kalubale da mawuyacin lokaci.

Barka da ranar haihuwa Mai girma Shugaban kasa…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button