Ya kamata Gwamnati ta jawo hankalin masu zuba hannun jari ne daga kasashen waje ba wai mu bi su can ba – Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya ce ya kamata Najeriya ta jawo masu zuba jari daga kasashen waje ba wai ta bi su ba.
Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake magana yayin tattaunawa ta kai tsaye ta X-space, mai taken ‘ParellelFact’ ranar Lahadi.
Kalaman nasa na zuwa ne a kan tafiye-tafiyen da Shugaba Bola Tinubu ya yi a kasashen waje don jawo hankalin masu zuba jari kai tsaye (FDI) zuwa kasar a ‘yan kwanakin nan.
Obi ya ce, “Ba wanda ke yawo don neman masu zuba jari daga kasashen waje. Masu zuba jari na kasashen waje kamar kudan zuma ne; idan kun ajiye zumar, za su tashi zuwa wurin. Ya kamata mu jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje kada mu bi su,” inji shi.
Amma, Shugaba Tinubu, a wata hira da ya yi da jaridar The Nation a ranar Lahadi, ya ce kasar na yin hulda da kasuwannin duniya- masu zuba jari na kasashen waje da na cikin gida.