Ya Kamata Talakan Najeriya Ya Farka Daga Bacci…
Yanzu haka ana kan kaddamar da Ɗan takarar Gwamna a garin Benin na jihar Edo, inda Ƴan jam’iyya, shugabanni, makaɗa da mawaka da Ƴan jagaliyya duk suka hallara domin wannan muhimmin taro.
A waje ɗaya Kuma Gov Nasiru Elrufai na jihar Kaduna yana cewa baza a buɗe kasuwanni ba saboda Korona, harma ya Ƙara da gwamma Ƴan kasuwa suyi bara da abude kasuwanni su kamu da Korona.
Abun lura anan shine, Ina Ƙungiyoyin sa Kai wato NGO’s?
Ina Ƙungiyoyin kare haƙƙin Ɗan Adam?Ina Ƙungiyar lauyoyi?
Ina masu kurin Boko na jihar kaduna?
Duk a zauna a kasa kalubalantar wannan ɗanyen hukunci.
Neman abinci fa farilla ne, Kuma Shima rights ne. Hana zuwa kasuwa Kuma bayan Korona tayi sauƙi to tauye haƙƙin tattalin arziki ne, wato (Economic rights).
Amma shiru kake ji babu Wanda ya kalubalanci hakan a kotu ko ɗaukar mataki na siyasa.
Kawai mutane suna zaune ana musu kisan mummuke.
Daga baya Kuma sai wani shaƙiyi ya fito yace Ɗan Arewa malalaci ne baya son Neman na Kai.
Talaka dai yasani babu Mai taimakonsa saifa idan ya taimaki kansa, ya nemi haƙƙinsa da doka da tsarin mulki ya bashi.
Bafa zai yiwu mu rushe tsarin mulukiyya da muka gada Kuma wasu yayan talakawa suci zabe su zaman mana fir’aunoni ba.
Idan kunne yaji jiki zai tsira..
B A Hussaini
Kano Nigeria
08/08/2020