Rahotanni

Ya kamata ‘Yan Jarida Su Rika Bibiyan Tarihi Yayin Gudanar Da Aikin Su Na Jarida, Inji Barrista El-zubayr Abubakar.

Spread the love

Idan zasuyi rubutu su maida hankali akan abubuwa da suka shafi haɗin kan ƙasa. Tun a zamanin mulkin Sojoji Ƴan Jarida sun bada gudumuwa don tabbatar Ƴanci da cigaban Ƙasa batare da tsoro ko fargaba. Yakamata Ƴan Jaridar wannan zamanin su dunga bibiyar tarihi don su dunga gyara ayyukan su.

Lauyan ya ƙara dacewa wajibi ne shigaba Buhari ya dunga tsawatarwa akan ayyukan da suka shafi ƙasa. Ko wani Minista da aka bashi aiki acijin kowacce wata shida a duba agani shin yayi abinda aka sakashi ? Idan bayyiba a tsawata mashi.

Lauyan yace Bai kamata ace Hukunar Dss sun saki Obadiah Mai lafiya ba yakamata su gudanar ƙwaƙwaran bincike akan hakan idan an same shi da laifi a gurfanar dashi a gaban kotu, yace sakaci ne mutum ya faɗi magana mai haɗari a barshi.

Barista Elzubayr Abubakar Lauya ne mai zaman kansa a Najeriya Mazaunin Jihar Kaduna.
Mai sharhine akan al’amuran yau da kullun kuma masanin dokoki ne da kuma Siyasa, Masanin tarihi da da dan gantaka tsakanin Ƙasashe (Diplomacy)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button