Labarai
Ya ku matasa Ku cigaba da kawo Sabbin dabarun kere-kere ~Pantami
Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani Dr. Isa Pantami, ya shawarci matasan Nijeriya da su ci gaba da kawo dabarun kere-kere da kasuwanci, musamman ma abin da ya shafi bangaren ICT.
A cewar majiyar kamfanin dillacin labarai na Najeriya, Pantami ya yi kiran ne a wajen bikin rufe gasar Hackathon Actinspace wacce NIGCOMSAT Limited suka shirya a Abuja.