Rahotanni

Ya Rasu Yayin Gabatar Da Sallar Idi A kano.

Spread the love

Wani bawan Allah mazaunin kano wanda Allah ya karbi rayuwarsa yayin da ake gabatar da Sallar Idi Karama a Masallacin Idi a unguwar Sharada da safiyar yau.

Lamarin ya auku ne yayin da yake cikin sallar wanda hakan ya sanya jama’a suka lura da cewa lallai bawan Allah din da alamu yakoma ga Mahaliccinsa ne.

Shaidun gani da ido sun tabbatar mana da faruwar al’amarin a yau din kenan.

Haidar H Hasheem wanda daya daga cikin Ma’aikatan mune ya samu zantawa da wadanda abun yafaru a gabansu inda suka baiyana masa yadda lamarin yafaru.

Wannan shine rahoto na biyu kenan damuka samu na Rasuwar mutum biyu a wurin Sallar a yau kenan inda dayan yafito daga wata jaha a cikin jahohin Najeriya

Muna rokon Allah ya kyautata makwancinsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button