‘Ya Ta Hauwa’u Aljanu Gareta, In Ji Mahaifiyar Matar Da Ta Kashe ‘Ya’yanta Guda Biyu Ta Hanyar Yi Musu Yankan Rago A Kano.
Da ake zantawa da mahaifiyar matar da ake zargi da kashe yaranta guda biyu, Hajiya Binta Ado Na Baba ta ce ‘Yar ta hauwa u tana da Aljanu.
Hajiya Binta Ado Na Baba tace hakika ‘Yar tata ta sha gaya mata cewa kullum cikin dare ana zuwa ana danneta kuma ana shaketa, ta fi wata uku bata barci, kullum cikin dare sai ta ringa ji ana mata wani gurnani irin Na dodanni.
Hajiya Binta Ado Na Baba ta ce da farko ban dauki maganar tata da muhimmanci ba, amma ina gaya mata cewa kullum in za ta kwanta ta ringa yin addu’a kuma ta ringa sanar da Mijin ta halin datake ciki.
Saidai mahaifiyar matar da ake zargi da kashe yaran nata guda biyu da take amsa tambayoyi ta ce tun randa ta aurar da ‘Yar tata shekara 6 da ta gabata suketa samun matsalolin rigin-gimu tsakaninta da Mijin nata, Wanda har hakan tasa dangin Mijin suka fara zargin lallai yarinyar ba lafiyarta kalau ba.
Hajiya Binta Ado Na Baba ta kara da cewa a ranar da abin ya faru tana gida a zaune sai taga yarinyar ta shigo, tace mata lafiya,,? Tace lafiya kalau.
Daga bisani sai ga Mijin nata ya shigo jikin sa duk jini yake cewa wai waya matar tasa tayi masa take cewa wai yazo ga ‘ya’yanta za su kashe ta, bayan ya zo sai ya tarar da yaran kwance cikin jini inda yafara zargin matar ce ta kashe su.
Da jin haka sai matar tace ta rantse da Allah ba ita ta ta kashe su ba, kuma bata san Wanda ya aikata kisan ba, ita dai ta gudo gida ne kawai saboda ba zata iya kwana a Gidan ba tsoro takeji.
Sauran bayani Na nan tafe.
Daga Kabiru Ado Muhd