Rahotanni

Ya zama dole kowanne Mutum ya Sanya Takunkumi a Fuskarsa~ Gwamnan Jahar Neja.

Spread the love

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Gwamnan Jahar Neja Abubakar Sani Bello Ya Sanya dokar Amfani da Takunkumin Fuska wato (Face Mask) ga Ko wanne Dan Jahar.
Gwamnan yace Kaddamar da Face Mask ne Yau a Gidan Gwamnatin Jahar dake Minna.

Inda Sani Bello yace daga yau Alhamis Kowa ya sanya Takunkumin Domin Kariya daga kamuwa da Corona Virus.
Sani Bello yace Jami’an Tsaro su kama duk Wanda bai sanya Takunkumin ba Ya Umarci Jami’an Tsaron Da su Shiga Lungu da sako na Jahar Domin Ganin wannan dokar Ta Rabbata.

Kawo yanzu dai Hukumar Kula da Cututtuka masu Yaduwa ta kasa NCDC tace mutane 2 ne ke Dauke da Corona a Fadin Jahar ta Neja.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button