Labarai
Ya zama wajibi Gwamnatin Jihar Kano ta dauki mataki kan wanda ya bankawa masallata Wuta a lokacin da suke Sallah ~Atiku Abubakar
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta dauki mataki tare da bincikar kan batun fashewar wani abu da ya faru a Larabar Abasawa a karamar hukumar Gezawa a jihar a lokacin da ake tsaka da Sallah
Atiku ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ta shafinsa X ranar Talata.
Idan dai za a iya tunawa, wani matashi dan shekara 38 mai suna Shafi’u Abubakar ya yi amfani da bam din mai wajen cinna wa masallacin Laraba Abasawa da ke karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano wuta a lokacin da ake sallar asuba.
Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf Yasha alawashin rattaba hannu domin hukuncin kisan ga wanda ya aikata wannan ta’asa.