Labarai

Yaci Kudin Makamai Har Naira Biliyan 157, EFCC Na Nemansa Ruw a Jallo.

Spread the love

Hukumar nan Mai Ikirarin Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC ta bada sanarwar Tana Nema Abubakar Hima, Wanda aka Baiwa kwangilar Kawo Makamai domin yakar Boko Haram da Sauran masu Tada kayar baya a Kasar nan.

Abubakar Hima dai asalinsa Dan Kasar Nijar ne, Kuma ya saba Yin kwangilar sayo makamai ga Kashen Larabawa, Hadda Najeriya.

Hima dai an bashi kwangilar kawo makamai na Zunzurutun kudi har Naira biliyan 157, a Shekarar 2017, Ya kawo Makamai marasa kyau kuma bai kawo Sauran makamanba, Sannan Yana zaune ne Gidan gwamnati dake Abuja (Villa).

Abubakar Hima, dai Aboki ne ga Shugaban Sojin Kasar Nan, Sannan yana da kyakkyawar alaka da mataimakin Shugaban Kasa, Shiyasa aka bashi wannan Kwangilar, duk da Ikirarin da Shugaban kasa Buhari yayi na, Ba’a amince abada Kwangilar makamai tsakani Gwamnati da ‘Yan kwangila ba, Sai dai Abada Tsakanin Gwamnati da Gwamnati amma sai Gashi an bada wannan kwangilar tsakanin Gwamnati da Dan Kasuwa.

Shi dai Hima, Sai da aka bashi kudin makaman sannan ya kawo wasu, sa6anin dan kwangila sai ya kawo abin an gwada yayi sannan gwamnati ta biya.

Tun wancan Lokacin dai ansan da wannan badakar Ba’a bincike shi ba sai Yanzu da Ibrahim Magu yabar Hukumar ake so a bincike shi, Wasu na ganin yanada daurin gindi a Gwamnati shi yasa aka barshi yaci gaba da zama A Gidan gwamnati duk da Irin Satar da tafka a Gwamnatin.

Sai dai Kwamitin da Buhari ya kafa Kan Binciken Zargin Magu ya Hango, Wata Takarda da Ibrahim Magu ya baiwa Abubakar Hima da Hukumar ta wanke shi daga Zargin Cinye kudin Makaman.

Dalilin Haka ne Shugaban Rikon kwarya na Hukumar ta EFCC na Yanzu ya Bada Cigiyar Abubakar Hima Dan Kasar Nijar da yayi sama da fadi da Zunzurutun kudin Makamai har Naira Biliyan 157.

Daman dai wasu ‘Yan Kasa na Zargin Ibrahim Magu da Sonkai a lokacin da yake rike da Hukumar ta EFCC.

Tun gabanni Kafa kwamitin na Binciken Magu, Mai Taimakawa Shugaban kasa ta Fuskar Watsa labarai Malam. Garba Shehu yace ‘Yan Najeriya zasu sha mamaki suji haushi Irin Abinda Kwamitin zai binciko Inji Shi.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button