Yadda Abba Gida-Gida Mai Rusau ya Ƙara Rugurguje Shatale-Shatalen Miliyoyin Naira

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf da gwamnatin sa na cigaba da rushe abubuwan da tsohon Gwamnan jihar, dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gina ba bisa ƙaida ba (a cewar su).
A yau ma, kamar yadda aka saba, an wayi gari da ruguje Shatale-Shatalen ƙofar gidan gwamnatin Kano.

Abisa ƙiyasi dai, anyi amanna cewar gwamnatin data wuce ta zare miliyoyin kudin jama’ar mutan Kano wajen gina gadar.

Ga Jerin yadda gadar ta kasance kafin da bayan yadda aka rushe wajen

Bayan an Rushe:







A yayin da ake wannan rusau, mutane daga cikin jihar da waje na ganin abin daya kamata kenan, yayin da wasu kuma ke ganin matakin yayi yawa.
Ga kadan daga cikin ra’ayi na mutane daban daban:
“Gaskiyar magana roundabout dinnan na kofar gidan gwamnati ya matse sosai… Kuma akan samu cunkoson ababen haka kusan kullum a wurin, musamman da yamma…Idan har an rushe shi ne domin fadadawa, da kuma canza fasalin wurin zuwa na zamani (i.e. underpass da overhead bridge, toh gaskiya wannan matakine maikyau...”
“Abun ya zama wani abu daban sai dai muyi fatan Allah ya kawo sauki”.
El-yaqb Bin Ahmad:
“Gaskiyane walla, wannan shataletalen yana daga cikin wurin da suke birgeni a jihar kano”.
“Ai da sauki tunda ba masallaci ko makabarta ko makaranta ya rusa baGwamna shi keda garinsa shi zai tsarashi Yadda yake bukata Abba mun yarda ya rusa duk inda bai masa ba”
Jama’a dai na cigaba da muhawara izuwa yanzu da muke haɗa rahoton nan game da rusau din.