Rahotanni
Yadda aka gudanar da bikin Ranar Bandaki ta Duniya jiya.
Hukumar Majalisar Dinkin Duniya, Itace ta ware ranar 19/11/ na kowacce shekara a matsayin ranar Bandaki ta duniya.
An ware ranar ne don Ilmantar da al’umma Musamman mazauna kauyeku yadda zasu rinka ta’ammali da Bandakunan su tare da koyar dasu yadda zasu zamanantar da Bayikansu zuwa dai-dai dana zamani, don gudun kamuwa da cututtukan da akan iya kamuwa dasu a Bandaki, kamar irin cutar::
-Sanyi.
-Gudawa.
-Amai da sauransu.
Jaridar Mikiya ta shiga garin Giwa Inda ta tarar da jimi’an kiwon lafiya na garin suna ta sintiri a cikin kasuwa don Ilmantar da al’umma.
Daga; Sunusi Danmaliki.