Yadda Dokar Bashi da Tinubu ya Sawa Hannu Zata Amfani Ƴan Najeriya Gamida Ƙaidojin Karɓa.
A yau litinin ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanyawa dokar cin bashi ta ɗalibai hannu a Abuja.
Sanya hannu a dokar, na ɗaya daga cikin alƙawurran yaƙin neman zaɓen sa da yayi na farfaɗo da ɓangaren ilimi a ƙasar.
Dokar daga yau, zata bawa ƴan ƙasa ɗalibai damar samun bashi daga gwamnatin tarayya domin samun damar yin karatu ko kuma bunƙasa rayuwar su.
Ga jerin yadda ƴan Najeriya zasu amfana wannan dokar ta cin bashin:
- Bashin bashi da kuɗin ruwa, saboda haka, ƴan Najeriya zasu biya iya adadin abinda suka ranta ne kawai.
- Dokar ta bashi, zata bawa ƴan ƙasa damar amsar bashin ne idan suna so suje makarantun gwamnati da suka haɗa da jam’ioi, makarantun fasaha da kuma makarantun gaba sa Sakandire a cikin gida.
- Dokar zata bawa ƴan Najeriya damar samun bashin daidai wadaida, batare da wariya ba daka iya tasowa daga wariyar jinsi, addini, yare, muƙami ko kuma yanayin halitta kowanni iri.
- Dokar tace, za’a iya bada kuɗin ne kawai idan za’a biya kuɗin makaranta
- Dokar ta sahale a ƙirƙiri “Bankin Ilimi” wanda za’a buɗe takanas domin samarwa yan Najeriya bashi domin karatu.
Ga jerin ƙaidojin da ƴan Najeriya zasu cika kafin samun bashin na ilimi:
1. Ɗalibin dake neman bashin, dole ne ya rubutawa shugaban bankin ta tsagin cibiyoyin bankin da za’a ƙirƙira, idan suka aminta da ka’idodi masu zuwa za’a sahale masa.
2. Ya zamto ya samu shaidar soma karatu a jam’ioi, makarantun fasaha da kuma makarantun gaba sa Sakandire mallakin gwamnatin tarayya ko na jiha cikin gida Najeriya.
3. Dole ne ya kasance wanda yake neman bashin, iyayen sa basa samun N500,000 a shekara guda.
4. Ɗalibi mai neman lamunin, dole ne ya kawo aƙalla masu tsaya masa guda biyu: dukkan su zasu kasance ma’aikacin gwamnati ne da bai gaza mataki na 12 a aiki ba, ko kuma wani lauya wanda yayi shekara 10 da soma aiki bayan kiran sa (Bar).
Ilimi nasa muhimmaci wajen cigaba da bunƙasa ƙasa ga kowacce ƙasa, saboda haka ana ganin wannan dokar ta lamuni da Tinubu ya sanyawa hannu ka iya zama wani mataki da zai kawo juyin juya hali a ɓangaren ilimi a Najeriya.