Yadda Matsalar Tsaro Ta Durkusar Da Ilimi A Arewa .

Ilimi a Yankin Arewa Musamman a wasu jahohin Ya cigaba da Cin Karo da Matsalolin Tsaro.
A kwanakin baya Ansha Samun Kai Hare-Haren ta’addanci a Wasu Makarantu, Misali:
A ranar 6 ga Watan July, 2013, a jihar Yobe Ankai Hari a Wata Sakandare dake cikin Garin Mamudo Na Garin Potiskum harin da, a Lokacin yasa an Rufe Makarantun Sakandare Na jihar Har Zuwa Watan September.
A ranar 29 September, 2013 an Kai Hari a college of agriculture dake Garin gujba Na jihar Yobe.
A Daren 14 April na Shekarar 2014, Aka Sace ‘Yan Matan Sakandaren garin Chibok Sama da 250 a jihar Borno, Zuwa yanzu Gwamnati Ta kubuto da Mafi Yawa Daga Cikin Su.
Haka Ma a Farkon Shekarar 2018 a Watan February an Sace ‘Yan Matan Sakandaren Dapchi Sama da 100 a jihar Yobe , Zuwa Yanzu Gwamnati Ta kubuto Dasu.
Yankin #AREWA Maso Gabas Yana Bukatar kulawa ta Musamman a, Bangaren ilimi.
Ranar #AREWA @ASOF2020