Labarai

Yadda Wasu Yara Suka Maƙale a Cikin Wani Gini Bayan Waya Ta Faɗowa Saman Ginin Su.

Spread the love

Masu ceton da suka fara isa wajen suna nan suna ta faman ganin sun ceto yaran yan uwa guda biyu da suka maƙale a cikin wasu ɓaraguzai a yankin Ikorodu dake jihar Legas.

Lamarin ya faru ne sakamakon faɗowar wata waya akan ɗakin da suke ciki saboda mamakon ruwan sama da aketa faman tsalawa kamar da bakin ƙwarya a yau asabar.

Lamarin maras daɗin ji dai ya faru ne a wani gini mai lamba 25 Alao a layin, Olainukan, Ishawo, Ikorodun jihar ta Legas.

Tuni dai Jaridar Vanguard ta ruwaito cewar, anyi ta zabga ruwa ne tun daga safiya har yamma , wanda hakan yasa wata waya dake kusa da wani gini ta faɗi kan ginin nan take kuma ta danne yara biyu a cikin ɓaragusai masu sarƙaƙiyar shiga.

Masu aikin ceto wanda yawancin su maƙota ne sun isa wajen a furgice, kum sun bazama neman yaran da shekarun su basu wuce 10 da tara a duniya ba.

Duk wani kokarin yiwa iyayen su magana ta waya yaci tura, domin ba’a same su ba yayin haɗa wannan rahoton.

To sai dai kuma, ko a daidai ƙarfe 3 na yamma nan an samu jinkiri, domin hukumar agajin gaggawa da kare haɗurra ta jihar Legas LASEMA da kuma yan kwana kwanar jihar, basu zo wajen ba duk da kiran da akayi musu na ujila.

Tuni dai aka shiga tsumayen su bayan kiran samfurin ujila.

Bugu da ƙari, duk wani ƙoƙari da akayi wajen tuntubar babban jami’in hukumar Dr. Femi yaci tura.

Karin bayani na nan tafe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button