Zamantakewa

Yadda Wata Mata Ta Cirewa Mijin Robarta Al’aura Bayan Yaci Amanarta

Spread the love

Matar mai suna Meirivone tace ansha faɗa mata yana kawo mata gida idan bata nan.

Tace ta taɓa kama zuwa gidan ta ga ɗan kamfai a ƙasa bayan tabar Marcelo a gida.

Ta yanke hukuncin hukunta mijin nata saƙaƙo ne, bayan ƙawar ta ta kira ta ta sanar da ita tagansa yana cin amanar ta.

Matar data karaɗe kafafen sadarwa na zamani kwanakin baya, dai ta auri yar bebin robanne, tun ba’a je ko ina ba kuma tace yana cin amanarta.

Ta sanar da mahaifiyar ta cewa, mijin nata ya sake cin amanar auren su kwanaki kaɗan da soma soyewar su.

Yar shekara 37 mai zargin masoyin tace tun daga lokacin da masoyin nata yaci amanarta, ta daina yarda ya kwanta mata akan gado, sai dai ya kwanta a ƙasa.

Hakan tasa, yanzu haka, ta cire masa mazantakar sa, ta hanyar datsewa da abu mai kaifi.

A cewar ta:

Ta yadda na gane yana cuta ta shine, ina zaune, sai naga saƙon ƙawata, in buɗe saƙon sai naga ta faɗamin cewar, sahibin nawa yana can yana cin amana ta”.

Ta ƙara da cewa:

a wannan dare, hankalina ya tashi, na furgice masa, nace yaje ya kwanta a kan kujerar tsakar falo“.

Kuma a cikin wani salon na hukunci, Meirivone tace, ta gutsurewa mijin nata mai suna Marcelo mazantakar sa.

Ga kalaman ta:

Wani samfurin farin robar mazantaka ne dashi mai tsawon inci 16. Kawai saboda fushi saina cire masa. Kuma daman na taɓa cire masa abarsa”. Inji Meirivone mai mijin roba.

Ta ƙara da cewa:

Ina tsoro wasu mata zasu iya taɓa masa mazantakar sa, zan ɓoye sa a cikin kabet ɗina, idan muka tafi gidan cin abinci ko kuma wajen kallo“. inji ta

Ta cigaba da cewa:

Tunda nayi masa haka, bazai ƙara shagala da son wata ba ko wata taso shi”.

Ita dai Meirivone ta nace akan saƙaƙo mijin roba, yaci amanarta a lokutan baya.

Tace:

“Na taɓa ganin wani ɗan kamfai jajawur a ƙasa, bayan na fita nabarshi a gida”.

Hakan ce tasa na gane cewar, ya soye da wasu matan, amma dana tambaye shi waye su sai yayi min shiru bai amsa ba.”

Allah ɗaya gari bambam.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button