Labarai

Yahaya Bello Ya Cire Dala $720,000 Daga Asusun Kogi Domin Biyan Kudaden Makarantar Yara -Shugaban EFCC.

Spread the love

Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya tura dala 720,000 daga asusun gwamnati zuwa wani ofishin canji kafin ya bar ofis domin biyan kudin makarantar da yaronsa gaba.

Olukoyede ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Talata a Abuja.

Ya ce, “Wani gwamna mai ci da yake ya san zai tafi ne kai tsaye ya dauko kudi daga gwamnati zuwa ofis, ya yi amfani da su wajen biyan kudin makarantar yara a gaba, dala 720,000 a gaba, da tsammanin zai bar gwamnati. Gida

“A jihar da ke fama da talauci kamar Kogi, kuma kuna so in rufe idona a kan hakan da sunan ‘Ana amfani da ni’. Wanene ke amfani da shi a wannan matakin rayuwata?”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button