Labarai

Yahaya Bello ya yi barazanar kamawa da gurfanar da wadanda suka ki amincewa da tsohon kudin Naira

Spread the love

A ranar Larabar da ta gabata ne kotun kolin ta yanke hukuncin cewa a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun naira na N1000, N500 da kuma N200 tare da sabbin takardun har zuwa Disamba 2023.

Gwamna Yahaya Bello na Kogi ya yi barazanar kamawa tare da gurfanar da wadanda suka ki amincewa da tsohuwar takardar Naira.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da sadarwa na Mista Bello, Kingsley Fanwo, ya fitar a Lokoja.

A ranar Larabar da ta gabata ne kotun kolin ta yanke hukuncin cewa a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun naira na N1000, N500 da kuma N200 tare da sabbin takardun har zuwa Disamba 2023.

Gwamnan ya bayyana a matsayin “ba za a amince da shi ba” da kuma “kaskantar da kai” ci gaba da kin amincewa da tsohon kudin Naira duk da hukuncin da kotun koli ta yanke.

“Wannan gwamnatin ba za ta tsaya kallon yadda wasu mutane da ‘yan kasuwa ke ci gaba da kin amfani da tsohuwar takardar Naira ba, ko da bayan hukuncin kotu da ta tabbatar da amfani da su.

“A gare mu, kin amincewa da tsofaffin takardun Naira, rashin biyayya ne ga hukuncin da Kotun Koli ta yanke, wanda bai kamata a bijirewa ba.

“Duk wanda ya ki amincewa da tsohuwar takardar naira, a kai rahoto ga jami’an tsaro da na gwamnati domin a kama su da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.

Gwamnan ya yi kira ga daukacin mazauna Kogi da su yi kokarin karbar tsoffin takardun kudi tun da bankunan kasuwanci suka fara ba su (tsohuwar takardar Naira) domin hada-hadar kasuwanci ta yau da kullum.

“A matsayinmu na masu kishin kasa, mutanen Kogi suma za su karba, saboda ba za mu iya ci gaba da kashe tattalin arzikinmu ba bayan kotun koli ta ba mu ‘yanci.”

“Saboda haka, gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti mai karfi don tabbatar da cikakken bin umarnin kotun koli dangane da amfani da tsofaffin takardu,” in ji Mista Bello.

Ya ce mambobin kwamitin sun hada da: kwamishinan kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na tattalin arziki na jihar; Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa.

Sauran su ne: Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu; mai baiwa jihar shawara kan harkokin tsaro da kuma Manajan Darakta na hukumar bunkasa kasuwanci ta Kogi (KEDA).

Gwamnan ya ce kwamitin ya tabbatar da cewa mazauna yankin sun ci gajiyar hukuncin da kotun koli ta yanke kan tsoffin kudaden Naira.

Gwamnan, ya taya ‘yan Najeriya murna kan hukuncin da kotun koli, babbar kotu a Najeriya ta yanke a tarihi.

Ya bayyana cewa a dalilin haka ne gwamnatin Kogi ta bi sahun sauran gwamnatocin jihohin kasar nan domin ci gaba da shari’ar, kuma suka yi nasara.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button