Labarai

Yakamata mu kafa wata gidauniya domin tallafawa ‘yan Maulidin da bom ya kashe a Kaduna ~Cewar Peter Obi.

Spread the love

Sakamakon harin da sojoji suka kai a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da isassun kudade ga sojoji, sauran hukumomin tsaro domin inganta ayyukansu.

Obi ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ziyarci wadanda lamarin ya rutsa da su a asibitin koyarwa na Barau Dikko da ke babban birnin jihar a yau ranar Talata, inda ya koka da cewa kawo yanzu kasar nan ta samu tashin bama-bamai 16 da sojoji suka yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 500, ba tare da wani abu da gwamnatin tarayya ta yi ba don dakile maimaituwar irin wadannan masifu ba.

Sai dai kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, ya jaddada bukatar gwamnati ta tallafa wa sojoji don ganin ba a sake afkuwa kamar tashin bama-bamai irin wannan ba.

Obi ya lura cewa isassun kudade ga sojoji shine mabuɗin wajen tinkarar matsalolin tsaro da ke addabar al’umma a wannan zamani.

Ya goyi bayan kiraye-kirayen a binciki harin da sojoji suka kai ta sama, kamar dai yadda ya bayar da shawarar kafa wata gidauniya da za ta tallafawa wadanda harin Tudun Biri ya rutsa da su, musamman wadanda lamarin ya rutsa da su marayu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button