Yakamata Nageriya ta kasance cikin Kasashe goma mafi Arziki na duniya domin muna da Kasar noma da Al’umma mai tarin yawa ~Cewar Kashim Shettima.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce babu wata hujja da za ta sa Najeriya ta kasa shiga cikin kasashe mafi arziki a duniya.
A cewar Shettima, tare da juyin juya halin shirin noma, Najeriya za ta iya kawo karshen rashin tsaro tare da rage talauci a tsakanin al’ummarta da ke karuwa.
Ya ce za a iya cimma irin wannan juyin ta hanyar amfani da fasahar kere-kere domin samun wadatar abinci a kasar, inji rahoton NAN.
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, yayin taron lacca karo na 13 na jami’ar Al-Hikmah.
Mataimakin shugaban kasar da yake jaddada darajar sahihancin sa hannun jari na kadarorin kasa da kuma basussukan kasa, ya ce, “Bisa la’akari da yawan filayen noma, albarkatun ruwa da kuma yawan bil’adama, Nijeriya ba ta da wani dalilin da zai hana ta shiga cikin kasashe goma mafi arziki na duniya a yau