Labarai

Yakamata ‘yan mata su rinka shiga aikin soja domin inganta tsaro a Nageriya ~Cewar Uwargidan Shugaba Kasa Oluremi Tinubu.

Spread the love

Uwargidan shugaban kasa a Tarayyar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, CON, ta bukaci shugabannin rundunar sojin Najeriya da su karfafawa mata gwiwa wajen shiga aikin soja.

Uwargidan shugaban kasar ta bayar da wannan umarni ne a jawabinta wanda uwargidan mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Shettima ta karanta a wajen taron tattaunawa na kwana daya na hedikwatar tsaro da ke dauke da taken, Samar da Nagarta ta hanyar inganta jinsi domin fuskantar kalubalen tsaro.

Uwargidan shugaban kasar, yayin da ta yaba wa shugabannin rundunar sojojin Nijeriya da suka shirya shirin, ta ce taron anyi shi a kan lokaci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button