Labarai
Yakamata ‘yan Nageriya su San ma’anar Sabuwar Rundunar SWAT.
Sufeto janar na ‘yan sanda, Mohammed a ranar Lahadi ya rusa rundunar‘ yan sanda ta musamman da ke yaki da fashi da makami kuma a ranar Talata, ya sanar da cewa, Runduna ta SWAT zata maye gurbin SARS. akwai wasu abubuwan da ya kamata ku sani game da Rundunar:
- Jami’an SWAT zasu tunkari kararrakin fashi da makami da sauran laifukan ta’addanci.
- Masu yuwuwar daukar matakin SWAT zasu fara horo a cibiyoyin horar da dabarun ‘yan sanda daban-daban a duk fadin kasar, mako mai zuwa.
- Wadanda zasu zama membobin zasu yi gwajin lafiyar jiki da kwakwalwa
- Za’a gudanar da gwajin lafiyar ne ta hanyar sabon sashin kula da bada shawara da tallafawa ‘yan sanda (PCSU).
- Tsoffin jami’an SARS ba za su taba kasancewa cikin sabuwar Rundunar SWAT ba.