Siyasa
‘Yan Arewa Na Shirin Yiwa ‘Yan Kudu Wayau Dan Ci Gaba Da Rike Shugabancin Najeriya A 2023, Inji Hadimin Shugaba Buhari’
Hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari dake bashi shawara akan yaki da cin hanci, Farfesa Itse Sagay ya bayyana cewa akwai wani kulli da Arewa ke yi dan dan yankin ya zama shugaban kasa a shekarar 2023.
Ya bayyana cewa masu kira da a zabi shugaban kasar da ya cancanta ai a kowane yanki akwai wanda ya cancanta.
Yace da ace masu kiran a zabi shugaban kasa saboda cancanta sun bari sai bayan yankin da bai yi shugabancin kasar ba ya kammala nashi shugabancin to da ya yadda dasu.
Yace wannan salon wayaune dan kawai wani bangare ya ci gaba da rike mulkin kasarnan domin kowane yanki na da wanda suka cancanta.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe