Labarai

‘Yan Arewa ne suka jawoma kansu wulakanci a kudancin Nageriya ~Inji Queen Janahstar

Spread the love


Wata matashiya ‘yar Asalin jihar Kano Mai Zama a kasar saudiyya Queen Janahstar CE ta rubuta Tace Idan jifa ya wuce kanka,
Babu inda wannan karin maganar ke aiki se agurin mallam Bahaushe. Bahaushe mai ban  haushi, kusan duk wani abu dayake cima Al’ummar mu tuwo a ƙwarya a wannan lokaci shine sakaci da rashin ɗaukar komi da muhimmancin da yakamata abashi, babban misali ta’addancin da aka dingayi wa fulani makiyaya a wasu yankuna a Arewa, a wannan lokacin babu irin kiran da marigayi Ali ƙwara baiyiwa gwamnatin Jihohi data Nigeria Kan ɗauki mataki akan al’amarin sabili da in Fulanin nan suka Fara ɗaukar mataki hakan baze haifar da ɗa mai ido ba amma sukayi burus da Al’amarin.

ba sena tsaya nayi jawabi akan abinda ke faruwa Game da matsalar ‘ƴan bindiga daɗi haɗi da kidnappers a arewacin kasar nan ba
Yanzun fisabilillah mutanen Arewacin munayiwa kanmu adalci???
Tsakanin jiya da yau abinda ya faru ga Mutanen mu Hausawa ƴan asalin arewa mazauna ƙasar yorubawa. Na irin kisan kiyashin da aka musu haɗi da ƙone dukiyoyin su da muhallan su..

Amma banga mutane suna maganarba  ba sai ƴan tsirarun mu Abin kuka da takaici shin wannan ba babban abin takaici bane? mu kanmu bamusan ƙimar junan mu ba inde abu ba garin mu yafaru ba a garin mu ma a ƙauyen mu toh be shafe ni ba kuma muna mancewa da karin maganar nan ta Mallam bahaushe yakeceaa  duk abinda yaci gimba toh bafa zai bar awai ba.
Kuma jeji baigama ci da wuta ba ba’a wa Bara Barka…
Bazaka taɓa sanin Arewa nada ƙarfin media ba se waccan matar Rahma sadau ta wallafa hoton tsiraici nan zakaga media ta ɗauka meyasa meyasa meyasa????

Akan abinda bashida wata ma’ana a gare mu shizamu maida hankali? Meyasa bazamu dage muyi yaƙi a social media ba saboda gyaran goben Mu??? Ko akan tumatir da Albasa wannan zamu iya gwada ƙwanjin mu balle ai maganar kayan abinci da sune

Daga Quee Janahstar 14-2-2021

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button