Labarai

‘Yan Bautar Kasa NYSC zasu Rabauta da tallafin Milyan bibiyu 2m

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta bai wa mambobin kungiyar masu yi wa kasa hidimar da za su himmatu ga harkar noma bayan sun yi shekara daya suna aiki kowanne kimanin N2m.

Babbar Daraktar, Cibiyar Nazarin Kayayyakin Samfuran Najeriyar, Dokta Patricia Pessu, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin yayin da take jawabi a wajen taron karawa juna sani kan karin kayayyakin amfanin gona ga ’yan yi wa kasa hidima 40 da aka zabo daga kananan hukumomi 16 na Jihar Kwara.

Pessu ta ce tuni wasu, ‘yan yi wa kasa hidiman biyu, waɗanda suka kammala bautar su a jihohin Oyo da Abia, sun fara cin gajiyar shirin, inda
Ta ce an zabo su ne daga rukunin karshe na wadanda suka samu horo a NSPRI.

T yi tir da karuwar yawan matasa marasa aikin yi a kasar nan sannan ta kara da cewa irin wannan damar tana jiran duk wani mai koyon aikin na yanzu wanda ya gabatar da kudiri mai kyau a karshen shekarar nan

Shugaban na NSPRI ya kara da cewa “idan aka sanya abubuwa cikin mahallin, matasan Najeriya marasa aikin yi na miliyan 13.9 sun fi yawan mutanen Rwanda da wasu kasashen Afirka da dama.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button