Tsaro

‘Yan Bindiga Sun Far Wa Al’ummomin Katsina, Sun Yi Garkuwa Da Mutum Hudu, Sun Ji Wa Daya Rauni.

Spread the love

‘Yan bindiga sun kai hare-hare da dama kan al’ummomin jihar Katsina, sun yi garkuwa da mutane hudu ciki har da Hajiya Asiya Dangiwa wacce’ yar uwa ce ga Manajan Darakta na Babban Bankin Mortgage na Najeriya na yanzu, Architect Ahmed Musa Dangiwa.

Mazauna yankin sun ce an yi garkuwa da Hajiya ne da sanyin safiyar ranar Laraba daga gidanta da ke garin Kankia, wasu ’yan bindiga da suka rufe fuskokinsu ne suka tafi da ita.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce ana ci gaba da kokarin ceto ta.

Kakakin ‘yan sanda wanda bai bayar da cikakken bayani ba, kawai ya ce,“ Zan iya tabbatar da satar da aka yi a Kankia amma muna kokarin ceto ta. ”

An kuma gano cewa wasu ‘yan bindiga a wasu hare-hare daban da safiyar Litinin, sun yi awon gaba da ma’aikacin Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a matakin farko, Alhaji Aminu Shaaibu daga gidansa da ke garin Mairuwa, cikin Karamar Hukumar Faskari da ke jihar.

Haka kuma an ce ‘yan bindigar sun raunata wani mutum da ba a san shi ba kuma sun yi awon gaba da wasu yara biyu na Alhaji Rabiu Maibulawus a karamar hukumar Dandume da ke jihar.

Cikakkun bayanan da ke faruwa game da lamarin har yanzu ba a san su ba a yammacin Laraba yayin da mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani game da lamarin ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button