Tsaro

‘Yan bindiga sun far wa ayarin kwamishina a Zamfara, sun kashe direba.

Spread the love

‘Yan bindiga da ke aiki a tsakanin Jihohin Katsina da Zamfara, a ranar Litinin, sun aukawa ayarin motocin Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar ta Zamfara, Hon. Abubakar Dauran, inda suka kashe direbansa a take.

Mutane da yawa sun jikkata a harin a cewar majiyarmu ta Dailypost.

Wakilinmu ya tattaro cewa lamarin ya faru ne lokacin da kwamishinan yake zuwa daga jihar Katsina inda ya je domin ya mika yara kanana 26 da akayi garkuwa da su ga Gwamnatin ta Katsina.

Lokacin da aka tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce’ yan bindigar ba su yi fito-na-fito da kwamishinan da tawagarsa kai tsaye ba.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma aka ba wa manema labarai a Gusau, babban birnin jihar, kakakin rundunar ‘yan sanda, SP Mohammed Shehu, ya ce wasu gungun’ yan fashi biyu ne suka atkawa ayarin.

Shehu ya roki jama’a da su taimaka wa jami’an tsaro a koda yaushe da bayanai masu amfani da za su iya kaiwa ga kame ‘yan ta’addan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button