Yan Bindiga Sun Hallaka Shugaban Kasuwa Har Lahira.
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu kisan gilla ne sun harbe shugaban kasuwar Harbour dake karamar hukumar Udu ta jihar Delta, Misis Freedom Odiete har lahira.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi, kuma wannan shine karo na uku da maharan ke neman rayuwarsa.
Mista Freedom dai wanda aka fi sani da Opito an yi masa kwanton bauna ne a yankin Ekete daidai mahadar babbar hanyar DSC a karamar hukumar.
A ‘yan bindigar suka yi masa dirar mikiya.
Daga nan ne suka harbe shi a kafadarsa ta dama inda ya yi karfin hali ya tsere amma suka sake bin shi har wurin da ya sami mafaka a kan hanyar Orhuwhorun suka ci gaba da harbinsa ba tare da kakkautawa ba.
ba zai rasa nasaba da wata cacar-bakin da ake yi tsakanin matasan yankin Ovwian da na Owhase kan mallakar wasu kasuwar.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar ta Delta, Onome Onovwakpoyeya ya tabbatar faruwar lamarin inda ya ce yanzu haka suna nan suna farautar makasan ruwa a jallo.
Daga:- Aliyu Adamu Tsiga