Tsaro
‘Yan Bindiga Sun Kashe Basarake A Kaduna.
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe Mai Garin Runji Alhaji Musa Abubakar.
Jaridar Daily Trust, ta ruwaito cewa ‘yan bindigan sun afka gidansa ne da sanyin safiyar yau Lahadi a garin na Runji da ke Ƙkaramar Hukumar Ikara ta Jihar Kaduna.
Dan mai garin, Suleiman Musa wanda shi ma mai gari ne a ƙkauyen Rafin Rogo, shi ya tabbatar da wannan lamarin.
Haka zalika Shugaban riko Na Ƙkaramar Hukumar Ikara, Salisu Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka kai jami’an tsaro ƙkauyen na Runji ya tabbatar da cewa za a gano wadanda suke da hannu a kashe mai garin kuma a hukunta su.
Ahmed T. Adam Bagas