Tsaro

‘Yan Bindiga sun kashe Hakimi, sun sace tsohon shugaban jam’iyyar PDP, da wasu Mutum bakwai a Zamfara.

Spread the love

‘Yan bindigar wadanda suka afka wa kauyen Gwaram, karamar hukumar Talatan Mafara a jihar Zamfara da sanyin safiyar ranar Litinin tare da baburan hawa, sun kuma yi awon gaba da mutane takwas da suka hada da matar shugaban garin da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na mazaba, Musa Makeri.

‘yan bindiga da ake zargin‘ yan fashi ne sun kashe Hakimin kauyen Gwaram, karamar hukumar Talatan Mafara a jihar Zamfara.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara, Shehu Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin a Yau Alhamis.

Mohammed ya ce an harbe shugaban kauyen ne bayan ya ki yarda a sace shi daga ‘yan ta’addan sannan ya ce ya fi son a kashe shi a cikin garinsu maimakon a dauke shi zuwa daji.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button