‘Yan Bindiga sun kashe Hakimi tare da sace mutun takwas 8 a Zamfara.
Wani dan asalin yankin, Usman Gwaram ya shaida wa kamfanin labarai na Analyzer cewa, ‘yan fashin da suka zo kauyen da misalin karfe 3 na safiyar Litinin da ta gabata sun so yin garkuwa da basaraken ne amma ya ki bin su.
A cewar Usman, basaraken kauyen ya fadawa barayin cewa, ya gwammace ya mutu da ya bi su zuwa maboyarsu.
“Lokacin da ‘yan fashin suka fahimci haka, basaraken kauyen bai ba su hadin kai ba sai suka sare shi da adda wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa”.
“Daga baya sun koma wasu gidaje inda suka yi garkuwa da mutane takwas ciki har da matar Hakimin yankin, Hajiya Sharifa da tsohon shugaban PDP na yankin, Alhaji Musa Makeri”. Inji Usman.
Munyi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Mohammed Shehu Amma ya ci tura saboda bai dauki wayar ba.