Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mafarauta 17 Tare Da Yin Garkuwa Da 25 A karamar hukumar Jibia ta Katsina.

Spread the love

A ranar Larabar da ta gabata ne ‘yan bindiga suka kashe wasu mafarauta goma sha bakwai har lahira tare da yin garkuwa da ashirin da biyar a dajin Tsayau dake cikin karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

Daya daga cikin shugabannin mafarautan na yankin Jibia, wanda bai so a ambaci sunan sa ya shaida wa Jaridar RARIYA ta waya cewa abun ya faru a gusanci Tsayau.

Majiyar RARIYA ta kara da cewa rashin sani ya sanya mafarautan suka afka maboyar yan bindigar, inda suka biyo mafarautan da babura, su kai ta harbin mai kan uwa da wabi, suka harbe mutane sha bakwai nan take, sun tafi da ashirin da biyar. Yadda muka tabbatar da an kashe sha bakwai din, wasu sun je wurin, domin duba dan Uwansu da aka Kashe, sun tabbatar mana da sun ga gawarwakin sha bakwai.

Shugaban ya ci gaba da cewa wadannan mutane ashirin da biyar sun nemi a ba su kudin fansa miliyan hamsin, mun ce masu ba mu da kudi sun ce mu je wajen gwamnati ta ba mu. Tun Farko mu da muka san wurin mun ba da shawarar kar a je wajen, da suka fada wajen iyalan yan bindigar da dabbobin suka firgita sakamakon hakan ne, su ka ta harbe mafarautan da yin garkuwa da wasu.

Ya ce cikin gawarwakin sha bakwai mutum daya aka rufe, wanda yan uwansa suka je dajin, kusa da gidajen yan bindigar. Muna kira ga gwamnati da ta taimaka mana wajen ganin an kubutar da mafarautan. Da marecen yau Lahadi sun kira sun ce ko ba mu bukatar su, saboda farko ma naira miliyan dari biyar suka nema a ba su a matsayin kudin fansa, inda muka ce mafarautan sun fito daga garuruwa daban daban na jihar Katsina, yana cewa idan ba mu kawo kudin za su kashe su.

Mafarautan sun fito daga garuruwan daga cikin garin Katsina da Tsagero da Abukur da Kanyar Uban Daba da Mashi da Fadi Gurje da Ku Tare da Dandagoro da Muduru da kuma kauyukan karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button