Tsaro

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mataimakin Kwamishinan’ Yan Sanda A Kuros Riba.

Spread the love

A Daren jiya ne da misalin karfe 1: Na dare wasu ‘yan bindiga suka kashe mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da ke aiki a lamba 73 PMF Squadron, Magumeri, jihar Borno, ACP Egbe Eko Edum.

Lamarin ya faru ne a garin Calabar, babban birnin jihar Kuros Riba.

Lamarin ya faru ne Laraba, 2 ga Disamba, da misalin 1:00 na dare.

Mamacin me suna,
GbeEgbe Eko Edum,

A cewar jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Irene Ugbo, ACP din ya zo Calabar ne don ganin dangin sa bayan sun kwashe lokaci mai tsawo amma sun iso da daddare.

Ugbo ya ce ‘yan sanda na zargin maharan‘ yan fashi ne.

Ta ce, “Ya sauka a garin kuma ya kirawo matarsa ​​ta dauke shi zuwa gida, a kan hanya ne wasu mutane da ba a san su ba suka far masa. Muna bincike kan lamarin, kuma dangin sun gano gawar daga wurin.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button