Yan Bindiga Sun Kashe Mutane goma a Kaduna.

Spread the love

Wasu ‘Yan Bindiga Dauke da gaggan Makamai sun Kashe a kalla Mutane 10 da Raunata Dadama a Jahar Kaduna.

Lamarin ya farune a garin Gora Gan dake karamar Hukumar Zangon Kataf a Kaduna.

Harin yayi sanadiyyar mutuwar mutane 10 Nan Take, Wayanda Suka samu Raunuka an garzaya dasu Babban Asbitin Gwamnati dake Zonkwa.

Wannan Harin dai Yazo ne Bayan Awanni 24 da Mahara suka kashe Mutane 20 a Wajen Biki a Garin Kukum dake Karamar Hulumar Kaura ta Jahar.

Idan Baku manta ba A Jiya Litinin ne dai Hafsan Hafsoshin Kasar Nan Laftanar Janar Tukur Burtai ya Sanar da Cewa Sunyi Nasara kan ‘yan Ta’adda a Yankin Arewa maso Yamnacin Kasar Nan.

Inda Burtai din Yayi Ikirarin Cewar ‘Yan Kasar nan ne Ke Kai Hare Hare kan ‘Yan Uwansu ba Bakin Haure ba.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *