Labarai
‘Yan bindiga sun kashe mutun 13 sun Kuma sace daliban Makaranta Sama da dari 100 a Jihar katsina.
Rahotanni da muke samu Cewa Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari a garin ‘Yar Kuka, kilomita biyar 5 daga karamar hukumar Kankara, a jihar Katsina, inda suka kashe mutane goma sha ukku 13 a daren shekaran jiya alhamis. A daren jiya juma’a sun shiga makarantar sakandire ta Kimiyya ta maza, da ke yammacin garin Kankara inda Suka sace daliban makarantar da dama. Rahotannin na Cewa kawo yanzu sama da mutun dari Suka sace duk da haryanzu Babu wani tabbacin adadin mutanen da aka sace Na daliban.