‘Yan Bindiga Sun kashe mutun ashirin 20 a jihar zamfara.
An dawo da kashe-kashen rayuka a Zamfara, ƴan bindiga sun hallaka mutum 20 a daren jiya
Rahotanni dake shigowa ta hanyar majiyarmu Hausa Daily Times daga ƙaramar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara na bayyana cewa a ƴan bindiga daɗi sun hallaka mutum 20 a ƙauyen Tungar Kawana dake gundumar Morai dake ƙaramar hukumar.
Lamarin ya faru ne a daren jiya Talata a cewar rahotannin inda a yau aka gudanar da jana’izar gawakin.
Har wayau a wani rahoton da Hausa Daily Timea daga birnin Gusau fadar jihar, biyo bayan yawan kashe kashe da ake samu yanzu a faɗin jihar wanda a kwanakin baya abubuwan sun lafa tun bayan yin sulhu da ƴan ta’addan na daji, al’umma sun fito kwansu da ƙwarkwata domin yin addu’o’i na musamman domin kawo ƙarshen rashin zaman lafiya a jihar.