Labarai

‘Yan Bindiga sun kashe mutun bakwai 7 karamar hukumar Igabi ta jihar kaduna.

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane bakwai tare da jikkata da dama a jerin hare-hare a kananan hukumomin Igabi, Giwa da Chikun da ke Jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Gidaje, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Yau ranar Alhamis.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun afka wa kauyen Gangi, da ke karamar hukumar Igabi, suna harbi lokaci-lokaci a wani abin da ya zama kamar aikin satar shanu kuma sun kashe mazauna garin hudu.

Wadanda aka kashe su ne Wada Sulaiman, Amiru Saidu, Yusha’u Mohammadu da Osama Abdulwahab, Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Gidaje, Samuel Aruwan, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar Alhamis.

Ya ce sauran mutum biyun da suka samu rauni a harbin bindiga kuma suna karbar magani a asibiti su ne Ibrahim Jibrin da Abdulhamid Suleiman.

Ya kuma kara da cewa a yayin samamen, ‘yan fashin sun kuma lalata gidaje uku na Mohammad Jibril, Salisu Ya’u da Idris Muhammad.

Ya ce wata motar daukar-kaya ce

A cikin duka, ‘yan fashin sun sace shanu 20 na wasu mazauna kauyen. A wani lamarin kuma, ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a kauyen Marke da ke cikin karamar hukumar Giwa suka kashe wani Rabiu Haruna,” inji shi.

A Kuriga da ke karamar hukumar Chikun, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kashe mutane biyu a kan hanyar Buruku da ta hada karamar hukumar Birnin Gwari.

Wadanda aka kashe din sun hada da Ibrahim Yahu Birnin Gwari da kuma Haruna Usman.

Ya ce wani mai suna Mansur Dada, ya samu rauni kuma yana karbar magani a asibiti.

Mista Aruwan ya ce gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya lura da rahotannin da bakin ciki, kuma ya aike da ta’aziya ga dangin wadanda aka kashe, yayin da ya yi addu’ar Allah ya jikan su.

Ya kuma yi fatan ‘yan kasa da suka jikkata su samu sauki cikin gaggawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button