Labarai

Yan bindiga sun kashe mutun Daya a jihar kaduna.

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin’ yan fashi ne sun kashe mutum daya a garin Megigginya da ke karkashin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna. ‘Yan fashin sun kuma harbe wasu mutum biyu, sun bar su da munanan raunuka. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:30 na daren Talata lokacin da ‘yan bindigar suka afka wa kauyen a kan babura suna harbi lokaci-lokaci.

Wannan harin ya faru ne ‘yan kwanaki bayan wasu‘ yan bindiga sun harbe wani shugaban dalibai kuma mai fafutukar #SecureNorth, Rabiu Auwal, a kan hanyar da ta hada filin jirgin saman Kaduna da tashar jirgin kasa ta Kaduna zuwa Abuja.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button