Labarai

‘yan bindiga sun kashe mutun Daya a wani sabon Hari a jihar katsina.

Spread the love

Rahotanni sun tabbatar Mana da cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin Fulani‘ yan fashi da makami ne sun kai wani sabon hari a garin Sabon Garin Bilbis da ke karkashin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina da sanyin safiyar Lahadi da misalin karfe 1:00 na dare Kamar yadda Katsina Post ta ruwaito,

‘yan fashin sun addabi jama’ar garin tare da kwashe kayayyaki masu muhimmanci da suka hada da kayan abinci da dabbobi na tsawon awanni ba tare da turjiya ba. ‘Yan fashin sun kuma harbe wani Mai suna Ashiru Umar a kafa, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa Bayan zubar jini Mai yawa sannan suka yi awon gaba da matarsa da yaro. Kashe-kashe da satar mutane don neman kudin fansa suna ci gaba a Katsina duk da karfafa tsaro a jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button