Labarai

‘Yan Bindiga sun kashe mutun daya sun sace Mutun Sha takwas 18

Spread the love

Rahotanni daga jihar Niger sun nuna Cewa Akalla mutum daya ne ya mutu, an yi garkuwa da 18, yayin da wasu da yawa suka samu raunuka daban-daban a lokacin da ‘yan bindiga suka far wa mutanen Kapana da ke Karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja.

Bayanai sun ce, ‘yan fashin sun afka wa mutanen ne a daren ranar Talata, suna harbin kan mai uwa da wabi.
Majiyarmu ta Daily trust ta tattaro cewa mazauna ƙauyen da abin ya shafa da sauran jama’ar da ke kewaye da su sun ƙaura zuwa wasu wurare.

Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Munya a majalisar dokokin jihar, Andrew Danjuma Jagaba, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi kira ga gwamnati da ta karfafa tsaro a yankin don dakile harin na gaba.

Ya kuma yi kira ga mutane da su kwantar da hankulansu, yana mai bayar da tabbacin daukar matakin gaggawa daga gwamnati.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, Wasiu Abiodun, ba a iya samun sa ba a lokacin da ake hada wannan rahoton.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button