Labarai

‘yan Bindiga sun kashe mutun Hudu 4 a jihar kaduna.

Spread the love

‘Yan bindiga a kan babura a ranar Laraba sun far wa kasuwar kauye a Galadimawa, karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna suka kashe wani shugaban’ yan banga da wasu mutum uku.

Daily trust ta tattaro cewa lamarin wanda ya faru da misalin karfe 2 na dare, ya haifar da annoba a kasuwar yayin da ’yan kasuwa daga kauyukan da ke makwabtaka da mazauna garin suka bazama don kare lafiya.
Hussaini Galadimawa, wani mazaunin yankin ya ba da sunan shugaban ’yan banga da aka kashe a matsayin Magaji Iyatawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, lokacin da aka tuntube shi, ya tabbatar da kisan shugaban’ yan banga.

ASP Jalige, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu rahoton halin da ake ciki ba game da mutum ukun da aka kashe a babbar hanyar amma ya jaddada cewa jami’an tsaro sun fatattaki ‘yan bindigar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button