‘Yan Bindiga sun kashe mutun Hudu 4 Kajuru ta Jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar ta kaduna Mista Samuel Aruwan, a ranar Alhamis, ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane hudu a fadin kananan hukumomin Igabi da Kajuru na jihar.
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a yammacin Alhamis.
A cewar sanarwar,
“Hukumomin tsaro sun bayar da rahoton cewa wasu‘ yan bindiga dauke da makamai sun far wa al’umman Nasarawa Kalgo da ke wajen garin Jaji, gundumar Rigachikun a karamar hukumar Igabi. ”
Mista Aruwan a cikin sanarwar ya kara da cewa, “‘yan bindigar sun afka wa kauyen da yawa, suka kashe wani mazauni Mai wuna, Harrisu Ibrahim.”
Kalaman nasa: “Hakazalika, wasu‘ yan fashi da makami sun kai hari yankin Kujama na karamar hukumar Chikun, kuma ‘yan banga na yankin sun fatattake su.
“Duk da haka, yayin da suke komawa maboyarsu, ‘yan bindigar sun kai hari a kauyen Janwuriya da ke cikin karamar hukumar Kajuru, suka kashe’ yan uwa biyu, Nuhu Ishaya da Yakubu Ishaya.”
Sanarwar ta kara bayyana kamar haka,
“A wani lamarin na daban,‘ yan bindiga sun mamaye Maraban Kajuru, shi ma a karamar hukumar Kajuru suka kashe wani mazaunin, kauyen Mai suna Samiru Na Ya’u.
“Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna damuwar sa da wadannan rahotannin, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda aka kashe, tare da aika sakon ta’aziyya ga dangin su. Ya kuma umarci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan abubuwan da suka faru. ”
An tsara za a ci gaba da sintiri a wadannan wurare, ”sanarwar ta ci gaba da cewa.