Labarai

‘Yan Bindiga sun kashe mutun Sha takwas 18 a kaduna tare sace Wasu da dama.

‘Yan bindiga sun kashe a kalla mutane 18 tare da yin awon gaba da wasu mutane da ba a bayyana yawansu ba, ciki har da karamin yaro, a kananan hukumomin Igabi da Chikun da ke Jihar Kaduna.

Majiyarmu ta tattaro cewa an kashe mutum bakwai a kauyen Anaba da ke Igabi yayin da aka kashe takwas lokacin da ’yan bindiga suka mamaye kauyen Barinje da ke karamar Hukumar Chikun.

Yayin da take tabbatar da hare-haren, Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ‘yan bindigar sun kuma kai hari a kauyukan Kwarten Rigasa, Kwarten Waziri da Kwarten Shaku da ke cikin karamar hukumar Igabi kuma a cikin lamarin, sun kashe wani Mai suna Danjuma Isa daga kauyen Ungwan Kanti da ke makwabtaka da su.

Gwamnatin jihar ta kara da cewa ‘yan bindigar sun mamaye kauyen Sanhu Makera a Igabi inda suka kashe wani manomi mai suna Yakubu Abdullahi, yayin da wasu da ba a san ko su waye ba a ranar Talata suka kashe wata Maryam Lash Tahir a kusa da rukunin gidaje na Minista, Millennium City, karamar hukumar Chikun.

Yayin da yake zantawa da daily trust mazauna Barinje sun ce ’yan bindigar sun kai wa kauyen hari ne da misalin karfe 6 na yamma a ranar Talata.

Hassan Silas ya ce mazauna garin da yawa sun koma garin Buruku, ya kara da cewa da yawa daga cikinsu sun samu raunuka na harbin bindiga yayin da ‘yan fashin suka sace wani karamin yaro suka yi awon gaba da shanu kusan 100.

Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ya ce a Anabe, ‘yan bindigar sun kuma kona gidaje, rumbunan ajiya da rumbuna tare da tserewa da shanu 20.

A cewar Aruwan, hare-haren da aka kaiwa wasu wurare masu sauki a kauyukan Anaba da Barinje da ke cikin kananan hukumomin biyu ya biyo bayan kisan da aka yi wa wasu ‘yan fashi da makami ne ta hanyar kai hare-hare ta sama inda aka bude musu wuta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button